Kwamishinar Zamfara Ta Aje Aiki Domin Mukamin Kwamishina A Jihar Imo

Kwamishiniyar Mata da Yara ta Jihar Zamfara, Rabi Shinkafi ta yi murabus domin karɓar muƙamin kwamishina a Jihar Imo.

Da ta ke baiyanawa Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN, Shinkafi ta ce “Na yi murabus a matsayin Kwamishiniya a Zamfara domin karɓar wani muƙamin a Imo.

“ina mai matuƙar godiya ga Gwamna Bello Matawalle da mai ɗakin sa, Hajiya A’isha Matawalle saboda alherin da su ke nuni da kuma bani damar yi wa Zamfara hidima a ɓangarori daban-daban.

“Duk wasu raɗe-raɗi da a ke yi a kan murabus dina ƙarya ne, aikin ƴan sharri ne . Ni akwai kyakkyawar alaƙa tsakani na da gwamna da mai ɗakin sa.

“Da shi gwamnan Imo Hope Uzodinma da Matawalle sun tattauna a kan muƙamin nawa kuma dukkan su dai ƴan jam’iyar APC ne,” in ji Shinkafi.

Labarai Makamanta