Kuskure Ne Tantance Tsoffin Shugabannin Tsaro – Sani

Tsohon Sanatan Jihar Kaduna Sanata Shehu Sani, ya soki lamirin majalisar Dattawa ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar Ahmad Lawan bisa tantance tsoffin Shugabannin tsaro da ta yi a matsayin jakadun Najeriya.

A cikin wani sakon da ya wallafa bayan an tabbatar da tsofaffin shugabannin hafsoshin soji a matsayin jakadu da shugaba Buhari ya nada, tsohon sanatan cikin raha ya ce za su “su gode wa Allah cewa ba su yi karo da majalisar dattawa a karkashin Bukola Saraki ba”.

Kwamared Shehu Sani ya shiga cikin ayarin masu sukar naɗin tsoffin Shugabannin tsaron ne, yayin da magoya bayan tsohon hafsan tsaro, Gabriel Olonisakin; tsohon shugaban hafsin soji, Tukur Buratai; tsohon Shugaban Sojojin Sama, Abubakar Sadique da kuma tsohon Shugaban Sojojin Ruwa, Ibok Ibas, suke murnar majalisa ta tantance gwanayen nasu.

‘Yan Najeriya da dama sun soki lamirin Shugaban ƙasa Buhari na bayar da sunayen tsoffin Shugabannin tsaron a matsayin jakadu, hakazalika Majalisar dattawa na cigaba da fuskantar suka sakamakon amincewa da ta yi dasu.

Tsoffin Shugabannin tsaron dai ana musu kallon ba su taɓuka komai ta fuskar samar da tsaro a Najeriya a tsawon wa’adin shekarun da suka ɗauka a fagen aiki. Inda da dama ake ganin sha’anin tsaro ya kara taɓarɓarewa har ake kallon gara jiya da yau.

Labarai Makamanta