Kuskure Ne Babba Dakatar Da Jarrabawar WAEC A Najeriya – Atiku

..

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya nuna rashin jin daɗinsa bayan gwamnatin Najeriya ta dakatar da gudanar da jarrabawar kammala sakandare ta WAEC a ƙasar.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa akwai hanyoyin da gwamnatin za ta iya bi wurin gudanar da jarrabawar ba wai ta dakatar da ita baki ɗaya ba.

Cikin hanyoyin da ya lissafo akwai batun amfani da manyan ɗakunan taro na ƙasar da makarantun firamare da filayen wasanni da sauran wurare domin amfani da su wurin gudanar da jarrabawar.

Ya bayyana cewa dama tuni sauran ƙasashen Afirka suka bar Najeriya a baya a fannin ilimi, ya kuma ce wannan yunƙurin na dakatar da jarrabawar zai iya jawo rikici a ɓangaren ilimi a ƙasar.

Ya yi gargaɗin cewa idan gwamnatin ƙasar ba ta bari an gudanar da jarrabawar ba, dubban mutane za su ƙetara maƙwafta domin zana jarrabawar.

Labarai Makamanta