Kungiyar Lauyoyi Ta Maka Buhari Kotu

Kungiyar Lauyoyin Nijeriya ta fara daukar matakin shari’a kan matakin shugaban kasa Muhammadu Buhari na tsawaita wa’adin Muhammadu Adamu a matsayin Babban Sifetan ‘Yan sandan Nijeriya.

Kungiyar na neman kotu ta fadi inda kundin tsarin mulki ya ba Buhari damar tsawaita wa’adin Adamu, bayan lokacin da doka ta dibar masa na shekara 35 a aikin gwamnati ya cika a ranar daya ga watan nan.

Ta ce akwai bukatar gaggawa na dawo da karfin doka a kasar a daidai lokacin da jami’an da ke tabbatar da dokar a cikin gwamnati suka kasa tsare hakkinta.

Kungiyar lauyoyin na kan matsayar cewa yanzu haka Adamu bai cikin jerin ‘yan sandan Nijeriya, bayan cikarsa shekara 35 yana aiki, tana mai bayyana kara wa’adin nasa a matsayin saba kundin tsarin mulki.

Labarai Makamanta