Kungiyar Kare Hakkin Musulmi Ta Yi Kiran Mayar Da 1 Ga Muharram Ranar Hutu

Kungiyar kare hakkin musulmai, MURIC ta bukaci gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi gyara a kan hutun da ta ke bayarwa, ta mayar da daya ga watan Muharram na shekarar musulunci a matsayin ranar hutu.

Kungiyar ta zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da bayar da hadin-kai wurin mayar da Najeriya kasar kiristoci inda ake kyale bukukuwan musulunci a bayar da hutu a lokacin na kiristoci.

MURIC ta bukaci Buhari ya daina bayar da hutun ranar 1 ga watan Janairu, ta ce kiristocin turawan mulkin mallaka suka kirkire hutun.

Kamar yadda takardar wacce darektan MURIC ya saki, Farfesa Ishaq Akintola, ya saki, kungiyar ta zargi yin shagulgulan bikin sabuwar shekarar kiristoci a matsayin rashin adalci ga musulman Najeriya kuma hakan bai yi daidai da dimokradiyya ba.

Labarai Makamanta