Kungiyar Kafafen Yaɗa Labarai Ta Koka Akan Matsalar Tsaro Dake Addabar Najeriya

Kungiyar gidajen yaɗa labarai Talabijin da Rediyo masu zaman kansu na ƙasa, ta koka dangane da halin da matsalar tsaro ke cigaba da addabar ƙasa musamman yankin Arewacin Najeriya.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata takardar sanarwa da ta fitar ranar Asabar wacce take ɗauke da sanya hannun Shugaban kungiyar na ƙasa Guy Murray Bruce da mataimakin shi Alhaji Tijjani Ramalan kuma aka rarraba ta ga manema labarai.

Kungiyar ta bayyana cewar halin da tsaro ke ciki yanzu a Najeriya tabbas abin tsoro da fargaba ne akan makomar kasar, domin lamari ne da ya faro a wani yanki guda sai gashi a yanzu ya mamaye ƙasar gaba ɗaya.
“Mun wayi gari ayyukan ta’addanci sun mamaye kasar, fashi da makami yin garkuwa da mutane rikicin manoma da makiyaya, babu wata kasa a duniya da za ta iya wanzuwa muddin tana fuskantar wadannan manyan kalubale”.

“Babu shakka fuskantar wadannan matsaloli na bukatar gudummuwar dukkanin bangarorin kasa baki daya, da kungiyoyin addini da yankuna, amma ya zamana wasu da ba sa fatan ganin ɗorewar kasar na cigaba da rura wuta fitina domin kawo cikas a ciki.

Kungiyar ta bayyana cewar tana da kyakkyawan imani da yakini akan cewa da akwai hikima ta Allah Ubangiji da ya haɗa mu wuri guda cikin ƙasa ɗaya mai mabanbanta al’umma, bisa ga haka muna kira da babbar murya ga dukkanin jama’ar Najeriya da su rungumi juna da tattalin zaman lafiya.

Kungiyar ta bayyana cewar a halin yanzu duniya na cikin wani yanayi na cigaba akan harkar yaɗa labarai, kuma a matsayin Ƙungiya ta kafafen yada labarai masu zaman kansu suna yin dukkanin kokari da haɗa kai da Gwamnati wajen wayar da kan al’umma muhimmanci na zaman lafiya da zaman tare.

Kungiyar ta kuma bayyana cewar za ta gabatar da bukatar ɗaukar nauyi na lokaci na kimanin rabin Biliyan wato naira Milyan 500 ga kwamitin Shugaban ƙasa mai yaƙi da cutar CORONA a gangamin yaƙi da cutar da za’a yi nan gaba a gidajen yaɗa labarai Talabijin da Rediyo a fadin kasar.

Daga karshe Ƙungiyar sun yaba da ƙoƙarin da jami’an tsaron kasar ke yi dare da rana na yaƙi da ta’addanci, inda suka yi musu kyakkyawar fata da addu’ar samun nasara a muhimmin aikin da ke gabansu.

Labarai Makamanta