Kungiyar ISWAP Ta Sanya Wa Jama’a Biyan Haraji A Borno

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno na bayyana cewar Manoma da mazauna garin Damboa da ke Jihar sun fara biyan haraji ga kungiyar nan mai ikirarin jihadi a Yammacin Afirka ta ISWAP.

Wani babban jami’in gwamnati ya shaida wa wakilinmu cewa a halin yanzu manoma na rayuwa karkashin jagorancin mayakan ISWAP a yankin Damboa.

Mayakan sun bai wa mazauna damar noma gonakinsu sannan su rika karbar haraji a matsayin zakka daga kowane manomi bayan sun girbe amfanin gona,” a cewarsa.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa manoman sun karbi wannan lamari hannu biyu domin sauki ne a garesu.

“A lokacin da kungiyar Boko Haram ke karkashin jagorancin marigayi Abubakar Shekau, ba su ko barin mazauna su fita gonakinsu, amma bayan ISWAP ta yi juyin mulki, ta bai wa mazauna damar fita gonaki amma da sharadin tilasta musu biyan haraji da kuma zakka,” a cewarsa.

Wani manomi mai suna Musa Mrusha, ya shaida wa wakilinmu cewa da yawa daga cikin manoma ba su son mahukunta su san halin da ake ciki.

“A lokutan baya, mayakan Boko Haram da dama sun kashe manoma masu tarin yawa a lokacin girbin amfanin gona a irin wannan lokaci. Amma babu wanda ya samu labarin faruwar irin haka a bana.”

“A farkon watan da ya gabata ne suka same ni a gona suka shaida min cewa idan lokacin girbin amfanin gona ya yi za mu ware musu nasu kason, kuma na amince da hakan har na cika wannan alkawari,” in ji Musa.

An ruwaito cewa, mayakan ISWAP wanda sun kafa tushe mai karfin gaske a Arewacin Borno, a baya bayan nan sun fara yaduwa a Kudancin jihar.

Daga ‘yan watannin baya zuwa yanzu, suna karbar haraji a hannun direbobi da manoma.

Wani fasinja mai suna Isma’il, ya ce mayakan sukan aiki direbobin su yi musu sayayyar kayayyaki a garin Biu, inda sun kafa wani shingen binciken ababen hawa a Sabon Gari, Yemantan, Ruga da wasu kananan tituna.

Ya ce “mayakan sukan buya a wasu wuraren da za su rika hangen motoci daga nesa tun kafin su karaso.

“Sukan yi shiga irin ta kakin soja wanda haka ke sa direbobi su tsaya a duk lokacin da suka tare su,” a cewarsa

Labarai Makamanta