Kungiyar CAN Ta Yi Kiran A Kama Dr. Gumi

Kungiyar Kiristocin Najeriya ta Ƙasa CAN tayi kira da babbar murya da cewar cikin gaggawa ba tare da ɓata lokaci ba Gwamnati ta yi gaggawar kama Malamin Addinin Musulunci Dr. Ahmad Abubakar Mahmoud Gumi, saboda kalaman shi da yake furtawa masu alaka da sha’anin tsaro na ƙasa.

CAN ta nuna damuwarta cewa shirun da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi na tsawon lokaci game da wasu maganganun kwanan nan da shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi ya yi, yana nufin amincewa da ikirarin nasa.

Daya daga cikin irin wadannan ikirarin na Gumi shi ne cewa sojoji kirista su ne ke kashe ‘yan Bindiga da sauran masu tayar da kayar baya a kasar nan.

Ƙungiyar kiristocin ta yi kira ga Gumi da ya janye “kalaman rashin kishin kasa da rarrabuwa” da aka alakanta da shi domin neman zaman lafiya da hadin kan kasar. Idan da Sheikh Gumi Kirista ne, da gwamnatin Buhari ta yi Allah wadai da kalamansa, sannan ta kame shi.

Sanarwar wacce babban sakataren Kungiyar CAN din, Joseph Daramola, ya sanya wa hannu ya ce, “Idan wani ya ce sojojin Kirista ne ke kai hari ga ‘yan bindiga, wannan mutumin ba ya fatan kasar nan da alheri kuma ba ya son yaki da ta’addanci da’ yan ta’adda ya ƙare cikin nasara.

“Ba za a iya ɗaukar hujjar murya ta Gumi da muhimmanci ba saboda ana iya shirya shaidar sautin murya da gangan don kafa hujja. Abu na biyu, ta yaya za mu iya tabbatar da amincin mutumin da ke zargin cewa sojojin Kirista ne ke kai hari ga garuruwa da ‘yan Bindiga?

“Wannan ikirarin da bai dace ba, baya ga bacin rai da raba kan rundunar sojin Najeriya da zai yi gida biyu ta ɓangaren addini, zai kuma bata martabar sojojin da ba kirista ba a matsayin wadanda basu jajirce wajen yaki da ta’addanci ba.

“Shirun da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi na tsawon lokaci daidai yake da amincewa da furucin Gumi mai hadari. Idan da za a danganta abin da Gumi ya fada ga shugaban kirista, da jami’an tsaro sun gayyace shi ko kuma su bayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo, kuma da Fadar Shugaban kasa ta yi Allah wadai da wannan shugaban na Kirista.

“Mun tuna yadda jami’an tsaro suka yi da kalaman Dr Obadiah Mailafia, Prophet Isa El-Buba da kuma na baya-bayan nan, Shugaban Katolika Dr Matthew Hassan Kukah sannan gwamnati ma ta yi martani. Shin da gaske muna da tsarkakkun da ba a tabawa a kasar yanzu?”

A gefe guda, Kungiyar matasan Ibo ta ‘The Ohanaeze Ndigbo Youth Council, OYC,’ ta bukaci a kama malamin addinin musulunci da ke kokarin yin sulhu da yan bindiga a arewacin Najeriya, Sheikh Ahmad Gumi nan take ba tare da ɓata lokaci ba.

Gumi ya fusata kungiyar ta Igbo ne sakamakon kwatanta shugaban Ibo, marigayi Dim Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu da ‘yan bindiga a hirar da aka yi da shi a BBC Pidgin.

Ojukwu ne ya jagorancin kabilar Ibo yayin yakin basasar Nijeriya da aka shafe shekaru uku ana gwabzawa wadda ta yi sanadin salwantar miliyoyin rayuka da tarin dukiya mara adadi.kuma na ganin laifin da Ojukwu ya yi ta yi kama da na yan bindiga.

Labarai Makamanta