Rahoton dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar ɗan takarar Gwamnan Jihar a karkashin jam’iyyar adawa ta PDP a zabe mai zuwa, Honarabul Isah Ashiru Kudan a ranar Laraba ya bayyana wasu Kudurori biyar da ya ke dasu ga al’umma da Jihar Kaduna wadanda yake ganin zasu dawo da martaba da mutunci ga mutane.
Manufar Ajandar ta shafi Tsaro, Noma, Lafiya da Ci gaban Matasa da Mata.
A wani zaman taron tattaunawa ta musamman da ke gudana a sakatariyar Kungiyar ‘Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ), reshen Jihar Kaduna don sanin manufofi da Kudurorin ‘yan takarar jam’iyyun siyasa wanda Kungiyar NUJ ta shirya, a ranar Laraba Ashiru ya yi karin bayani kan yadda zai tafiyar da manufofinsa domin samar da ci gaba da kuma taimakon al’umma, idan aka zabe shi a 2023.
Ya yi nuni da matukar damuwa, tabarbarewar tsaro da ke jawo rashin barci ga jama’a da kuma rarrabuwar kawuna da shakku a tsakanin kabilu daban-daban na jihar.
Dan takarar Gwamnan na PDP ya bayyana cewa talauci da rashin aikin yi da sallamar ma’aikata ba tare da biyan su hakkin su ba, na daya daga cikin wasu abubuwan da suka kara kawo matsalar tabarbarewar tsaro a Jihar.
Ya ce “a karkashin fannin Noma wanda shi ne mafi yawan ma’aikata, za a sa Manoman su koma Gona a tallafa musu da kayan amfanin Gona yayin da za a dawo da tallafin taki.
Ashiru ya yi alkawarin cewa za a farfado da mafi akasarin hukumomin Noma da aka yi watsi da su domin samun tallafin kasashen waje.
Yayin da yake yin alkawarin samar da asibitocin tantance marasa lafiya a kowane shiyya 3 na majalisar dattawan Jihar da ke karkashin lafiya, Ashiru ya lura da cewa galibin asibitocin da ake da su gine-gine ne kawai ba tare da kayan aikin da ya kamata a samar musu da su ba.
Dan takarar gwamnan ya ce “Jihar Kaduna tana da sama da mutane miliyan 9, da likitocin da basu wuce 200 ba, sabanin yadda duniya ke da nuni ga duk likita 1 na da damar duba mutane 600.
A bangaren ilimi, dan takarar PDP, ya yi alkawarin bullo da kwararrun tsarin ilimi, samar da kayayyakin aiki, tare da bada fifiko musamman ga Ilimin sana’o’in dogaro da kai.
Ashiru ya yi alkawarin kafa wani kwamiti da zai duba karin kudin makaranta a Jami’ar Jihar zuwa mataki mai sauki domin dakile matsalar fita ko barin karatu.
A yayin da ta yi alkawarin samar da daidaito ga daukacin ‘yan takarar, shugabar kungiyar NUJ ta Jihar Kaduna, Hajia Asmau Halilu a jawabinta na maraba, ta tabbatar wa dan takarar Gwamnan Jihar da kuma tawagar yakin neman zabensa cewa mambobin kungiyar za su jajirce wajen yin abin da ake bukata.
You must log in to post a comment.