Kudurin Zabe: Buhari Ya Aika Wasika Majalisar Kasa

Labarin dake shigo mana yanzu haka daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki amincewa da kudirin yin kwaskwarima ga dokar zabe ta 2021, kamar yadda Majalisa ta nema.

A wata wasika da ya aikewa shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, shugaban ya ce halin da kasar ke ciki ba zai ba shi damar sanya hannu kan kudirin ba.

Daga cikin dalilan kin amincewa da kudirin, shugaban ya bayar da misali da kudaden gudanar da zaben fidda gwanin kai tsaye, kalubalen tsaro na sa ido kan zaben, take hakkin ‘yan kasa da kuma mayar da kananan jam’iyyun siyasa saniyar ware.

Buhari ya ce ya samu shawarwari daga ma’aikatu da sassa da hukumomin gwamnati da abin ya shafa, sannan kuma ya yi nazari sosai kan kudurin bisa la’akari da abubuwan da ke faruwa a Tarayyar Najeriya a halin yanzu.

Labarai Makamanta