Ku Yi Gaggawar Ceto Sauran Fasinjojin Jirgin Abuja – Buhari Ga Jami’an Tsaro

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Buhari ya umarci jami’an tsaro su sake jajircewa wajen ceto sauran fasinjojin jirgin kasa da aka yi garkuwa da su a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, shugaban ya ce, ya yi farin ciki fasinjojin da aka sako, kuma za a ci gaba da kokari wajen ganin sauran mutanen da ke hannun ‘yan bindiga sun dawo gida cikin koshin lafiya.

A ranar 28 ga watan Maris din 2022, ‘yan bindiga suka tare jirgin a hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja, tare da awon gaba da fasinjoji masu yawa.

Kakakin shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu, ya ce gwamnati na kokari don ceto sauran fasinjojin 51 ko sama da haka da ake tunanin har yanzu na tsare.

Labarai Makamanta