Ku Yaki Talauci Da Rashin Tsaro Domin Dawo Da Natsuwa Ga ‘Yan Najeriya – Sarkin Musulmi

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci na Nijeriya, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya bukaci shugabanni a kasar nan da su ji tsoron Allah su tallafa wa ‘yan kasa saboda yanayin wahalar da ake ciki.

Abubakar a sakonsa na Sallah a Jihar Sakkwato, ranar Talata, ya ce wahalar da ake ciki a Kasar nan abin damuwa Ce matuka, ya kara da cewa ana bukatar matakan da suka dace don magance ta.

“Shugabannin Nijeriya na bukatar kara dabarun daukar wasu matakai don magance matsayinmu na talauci da rashin tsaro, domin hakan zai kara tabbatar da hadin kai da zaman lafiya da ke cikin kasar.

“Yanzu abin da ke faruwa ba labari ba ne gaskiya ne, mutane suna matukar bukatar jajircewar shugabanni don magance yawan talauci, rashin tsaro, da yunwa a tsakanin sauran kalubale masu yawa.

“Saboda haka, ya kamata shugabanni su ji tsoron Allah su sauke nauyin da ke kan su domin bunkasa yanayin rayuwar ‘yan Nijeriya, ’in ji Sultan.

Shi ma a nasa sakon na Sallah, Gwamna Aminu Masari na Jihar Katsina ya yi kira ga shugabanni da su karfafa zaman lafiya da hadin kai a tsakanin kasashe daban-daban ba tare da la’akari da kabilanci, addini, da siyasa ba.

“A matsayinmu na shugabanni, dole ne mu jaddada abubuwan da za su inganta zaman lafiya, hadin kai, da kuma zama tare tsakanin mutane,” in ji shi.

Gwamnan ya jaddada cewa babu kasar da za ta ci gaba a cikin yanayi na bambance-bambance da rikice-rikice.

Ya ce, ana bukatar hada karfi wuri guda don tunkarar kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta a yanzu kasancewar gwamnati ita kadai ba za ta iya yin hakan ba.

Daga jihar Kano, Gwamna Abdullahi Ganduje ya bukaci Musulmi da su yi addu’ar zaman lafiya, hadin kai, da kwanciyar hankali a kasar.

Ganduje ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su ci gaba da yin addu’a game da tayar da kayar baya, fashi da makami, satar mutane, da sauran nau’ikan aikata laifuka a kasar nan.

“Ina kuma yin kira ga Musulmi da su ci gaba da tsayawa tsayin daka tare da bin son gaskiya da zaman lafiya, ” in ji shi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply