Ku Taya Mu Tsare Ofisoshinmu: Rokon INEC Ga ‘Yan Najeriya

Shugaban Hukumar zaɓe mai zaman kanta Farfesa Mahmood Yakubu ya roƙi al’ummar Najeriya su taimaka wurin kare kadadrorin hukumar gabanin babban zaɓen ƙasar mai zuwa.

Hakan na zuwa ne bayan hare-haren da aka kai wa wasu ofisoshin hukumar a baya-bayan nan.

Farfesa Yakubu ya bayyana hakan ne a lokacin da ya gana da ƙungiyar dattijan yammacin Afirka, a ofishinsa da ke Abuja, a ranar Litinin.

Shugaban na INEC ya ce babban abin da ake fargaba gabanin zaɓen mai zuwa shi ne matsalar tsaro.

Ya ce “an kai hari a ofisoshinmu a ƙananan hukumomi uku, a cikin ƙasa da mako uku, irin waɗannan hare-hare guda bakwai ke nan aka kai a cikin wata huɗu.”

Ya ƙara da cewa “nauyi ne a kanmu baki ɗaya mu haɗa hannu domin kare su. Dole ne a daina kai hare-haren kuma wajibi ne a kamo tare da gurfanar da masu alhakin kai harin.”

Sai dai ya tabbatar wa al’umma cewa za a gudanar da zaɓen kamar yadda aka tsara, duk da barazanar tsaro da ake fuskanta.

Labarai Makamanta