Ku Sanya Najeriya Cikin Addu’o’i Lokacin Easter – Mr LA

Honorabul Lawal Adamu Usman (Mr LA) tsohon dan takarar majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya ya taya daukacin al’ummar kirista murnar bukin ranar Easter.

Mr LA ya kuma yi kira na musamman ga daukacin mabiya addinin kirista da su cigaba da yiwa kasar addu’ar samun dauwamanmen zaman lafiya yayin shagulgulan bikin Esther.

Mr LA ya bayyana hakan ne a Kaduna yayin ganawa da manema labarai Jim kadan bayan ya kaiwa wata ziyara a cibiyar kula da marayu, kananan yara da marasa karfi a nan garin kaduna.Daga karshe Ya kuma yi kira ga sauran shuwagabannin addini akan su cigaba da nunawa mabiyan su muhimmancin yiwa kasa addu’a a koda yaushe.

Labarai Makamanta