Ku Mutunta Juna A Yayin Gudanar Da Yakin Neman Zabe – Gargaɗin Buhari Ga ‘Yan Takara

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya fada wa ‘yan takarar cewa zaben 2023 ya fi gaban zabe dama ce ta bautawa ƙasa Najeriya.

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya nemi ‘yan takarar a zaben 2023 su guji keta rigar mutunci da tunzura jama’a a yakin neman zabensu.

Shugaban ya yi gargadin cewa karuwar labaran bogi da karkatattun labarai na ci gaba da zama gagarumar barazana ga tsarin dimokradiyyar Najeriya.

Ya ce labaran bogi na dauke hankali daga yin yakin neman zabe bisa manufa maimakon haka sai a yi ta kwarzanta yiwuwar cin mutuncin mutane da zaga-zage da harzuka mutane.

Muhammadu Buhari ya yi wannan jawabi ne a wani sakon bidiyo da ya gabatar a taron sa hannun ‘yan takarar shugaban kasa don tabbatar da zaman lafiya a zaben 2023.

Labarai Makamanta