Ku Kare Kanku Daga ‘Yan Bindiga – Ministan Tsaro

Ministan Tsaron Nijeriya Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya, ya bukaci ‘yan Nijeriya su samu kwarin guiwar kare kansu daga hare-haren ‘yanbindiga da kasar ke fama da shi.

Da yake magana da ‘yanjarida a ranar Laraba, kan aikin tantance sabbin shugabannin tsaro da majalisar wakilai ke yi, Magashi ya bayyana wadanda suka sace daliban da aka yi a makarantar sakandiren kimiyya ta Kagara a matsayin raggwaye.

Ya ce ‘yan Nijeriya na da alhakin tabbatar da cikakken tsaro a tsakaninsu, yana mai yin watsi da ikirarin da wasu ke yi na a ba ‘yan Nijeriya damar su mallaki makamai don kare kansu.

Sai dai bayanan na ministan sun haifar da surutai Tsakanin ‘yan Najeriya inda mafi yawan jama’a ke ganin kalaman ministan tsaron a matsayin gazawar Gwamnati.

Labarai Makamanta