Ku Daina Ɗaukar Zaɓe Tamkar Yaƙi – Kiran Jonathan Ga ‘Yan Siyasa

Tsohon Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan ya shawarci ‘yan siyasa da su daina daukar zabe tamkar juyin mulki ko kuma yaki, maimakon goya wa wanda ya samu nasara baya domin sauke nauyin da jama’a suka dora masa.

Jonathan da ke jawabi wajen bikin cika shekara guda da hawa karagar mulkin Gwamnan Jiharsa ta Bayelsa Douye Diri ya ce a Najeriya musamman a matakin kasa an fahimci yadda aka dinga sauya gwamnati ta hanyar juyin mulkin soji abin da ke haifar da gaba ko da an samu nasara ko ba’a samu ba.

Tsohon shugaban ya ce dimokiradiya ta bada damar amfani da doka, saboda haka babu dalilin da ‘yan siyasa zasu dinga amfani da hanyar zabe da sauya gwamnati kamar yadda sojoji ke shirya juyin mulki.

Jonathan ya ce abin sani kawai shine, a karshen kowanne zabe, ana bukatar Jam’iyyun siyasa da su hada kai wajen goyawa wanda ya samu nasara baya, yayin da shi kuma zai hada kan su domin tafiya tare.

Ya ce shi bai ga laifin idan shugaban kasa ko gwamna daga wata Jam’iyya ya dauko wani da ya ga ya kware daga jam’iyyar hamayya wajen nada shi minister ko kwamishina, domin kuwa kasa za’a yiwa aiki.

Labarai Makamanta