Kowane Gwamna Masoyin Buhari Ne A Jiharsa – Gwamna Bala

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya amsa cewa mutanen jiharsa magoya bayan Shugaba Muhammadu Buhari ne. Mohammed, wanda daya ne cikin shugabannin PDP ya ce “kowa a jiharsa magoyin bayan Buhari ne” a wurin kaddamar da kamfanin Kolmani Integrated Development Project a jihar Bauchi a ranar Talata, 22 ga watan Nuwamba.

Tare da shugaban kasar a wurin kaddamarwar akwai Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan; direkta janar na kwamitin kamfen din shugaban kasa na APC, Simon Lalong, Ministan sadarwar da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Pantami da wasu.

Taron shine kaddamar da hakar danyen man fetur karon farko a arewacin Najeriya a hukumance, wanda aka gano a iyakan jihohin Bauchi da Gombe duk a arewa maso gabas.

Gwamnan jihar Bauchi ya nuna rashin jin dadinsa da halin dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar, na yin watsi da shi. Idan za a iya tunawa Mohammed ne mataimakin shugaban kwamitin kamfen din shugaban kasa na PDP a zaben 2023 a arewa maso gabas.

Gwamnan ya yi ikirarin Atiku baya goyon bayan tazarcensa a jihar Bauchi kuma bai ziyarce shi ba bayan zaben fidda gwani kamar yadda ya ziyarci sauran yan takara.

Labarai Makamanta