Kotun Tarayya Ta Bada Umarnin Kama Shugaban PDP Kan Sauya Dan Takara A Borno

Babbar kotun tarraya dake Abuja ta bukaci akama shugaban jmaiiyar PDP da Farfesa Iyochia Ayu da Wani Dan Jamiyyar PDP Muhd Umara Kumalia akan zargin yin takardun bogi wadadan suka Kai ga sauya Asalin Dan takaran Dan majalisar Dattawa a shiyyar Borno ta tsakiya Hon Jibrin Tatabe.

Kotun ta ce abinda shugaban Jamiyar PDP da wasu shugabannin Jamiyar ya saba kaidar da kundin TSARIN Mulkin PDP, Wanda ya kamata a hukuntasa kamar yadda Doka ta tanadar.

A wani bangare ita ma Babbar tarayya dake Maiduguria ajihar Borno, ta tabbata da cewar Hon Jibrin Mustapha Tatabe shi ne halarataccen Dan takaran Dan majalisar Dattawa daga Borno ta tsakiya.

A ranar 9 ga watan janairu ne ta yanke Wannan hukunci inda tace Jibrin Tatabe shine Dan takaran jammaiaya PDP a shiyyar Borno ta Tsakiya a zaben Mai zuwa na 2023.

Mai sharia na babbbar Kotun Jude H Dagat shine ya yanke Wannan hukunci Wanda hakan ya kawo karshen Cece kuce da aka dade ana Yi a akanwanna. Kujera ta PDP.

A cikin wata Sanarwa da maitaimaka masa a bangaren yada labarai Walid Aminu Yakudima ya fitar ta ce Jibrin Mustapha Tatabe ya fuskanci rashin adalci na tsawon lokaci akan Kujeran, ya nuna Farin ciknsa akan matakinda kotun ta dauka saboda Yana Mika godiyarsa ga Allah da Kuma wannan Koutu Mai Albarka..

Walid ya ce Tatabe ya ce wannan ba nasarar sa bace kawai Nasara ce ga daukancin Alummar jihar Borno ta tsakiya wadadan suka Daura masa.wanna Nauyi na wakilci.su .saboda sun tabbatar da kwarewarsa wajen shugabanci.

Labarai Makamanta