Kotu Ta Yi Fatali Da Karar Da Gwamnatin Katsina Ta Kai Mahadi Shehu

Rahotanni dake shigo mana daga jihar katsina na bayyana cewa a ranar Talatar data gabata wata Kotun majestare dake zamanta a babban birnin jihar ta kori karar da gwamnatin jihar ta kai shahararren ɗan kasuwar nan Dr Mahdi Shehu.

Kotun karkashin jagorancin mai shari’a Abdulkarim Ahmed Umar ta sallamin karar da Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar ya shigar kan Mahadi Shehu kan zarge-zargen da sukayi masa ciki harda zargin aikata ta’addanci.

Hakan ya biyo bayan kiran da mai shigar da karar ASP Kabir Muh’d yayi ga kotun kan ta kori karar sakamakon rashin gamsassun hujjoji.

Wannan dai shine kusan kashi na hudu da Dr Mahadi Shehu ke samun nasara akan gwamnatin jihar Katsina ƙarkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari bisa zargin da yake yi mata na almubazzaranci da barnatar da dukiyar jama’a.

Labarai Makamanta