Kotun daukaka kara a birnin tarayya Abuja ta yi watsi da karar da Sanata Dino Melaye ya shigar na kallubalantar nasarar Sanata Smart Adeyemi a matsayin wanda ya lashe zaben sanata ta mazabar Kogi ta Yamma.
Alkallan kotun uku dukkansu sun amince a kan watsi da dalilai bakwai da aka yi la’akari da su yayin watsi da daukaka karar ta Melaye.
Kotun ta jaddada hukuncin da Kotun Zaben Majalisa da ke Abuja ta yanke a ranar 10 ga watan Yunin 2020 wacce ta tabbatar da nasarar Adeyemi kamar yadda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC ta sanar.
You must log in to post a comment.