Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanín PDP Na Sanatan Kaduna Ta Tsakiya

Babbar Kotun tarayya dake zama a jihar Kaduna ta rushe zaben fidda gwanin jam’iyyar PDP na ɗan takarar Sanata a mazaɓar Kaduna ta tsakiya kan sabawa dokoki da ƙa’idoji.

Kotun karkashin jagorancin mai Shari’a Muhammad Umar ta umarci jam’iyyar PDP ta sake shirya sabon zaɓe cikin makwanni biyu wato kwanaki 14.

Hukuncin Alkali Umar na zuwa ne biyo bayan ƙarar da ɗaya daga cikin yan takarar da suka nemi tikitin sanatan, Ibrahim Usman, ya shigar gaban Kotun, inda ya kalubalanci yadda aka gudanar da zaɓen.

Lawal Adamu, shi ne aka ayyana a matsayin wanda ya lashe tikitin da kuri’u 99, inda ya lallasa babban abokin hamayyarsa na kusa, Ibrahim Usman, wanda ya samu kuri’u 84 kuma ya zo na biyu.

Musa Bello da Inuwa Ahmed sun tashi da kuri’u 43 da 15 kuma suka zama ma na uku da na huɗu a jere, yayin da Usman Muhammed da Hajiya Shehu suka zo na biyar da na shida da kur’iu biyu da biyar kamar yadda kwamitin zaben ya sanar.

Saboda rashin gamsuwa da sakamakon, Ibrahim Usman, ta hannun Lauyansa, Samuel Aung, ya roki Kotun ta soke zaɓen bisa hujjar aringizon kuri’u.

Ya nemi Kotun ta ba da umarnin canza sabon zabe wanda za’a baiwa kowane ɗan takara damar gwada sa’arsa a sahihi kuma nagartaccen zaɓe.

Alƙalin Kotun mai shari’a Umar ya yi fatali da hujjojin wanda ake kara kana ya nuna gamsuwa da na mai ƙara, sannan ya ba da umarnin sake zaɓe nan da mako biyu.

Labarai Makamanta