Kotu Ta Sanya Ranar Saurarar Karar Zakzaky

Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja ta zabi ranar 19 ga Junairu, 2022 matsayin ranar sauraron karar da Shugaban Kungiyar Shi’a a Najeriya Sheikh Ibraheem El-Zakzaky da matarsa Zeenah suka shigar kan hukumar DSS da Antoni Janar na tarayya.

Alkalin Kotun mai Shari’a Inyang Ekwo, ya zabi wannan rana ne domin baiwa hukumar DSS da ministan shari’a damar martani kan zargin take hakkin dan Adam din da Malamin ya shigar kansu.

Sheikh Ibraheem El-Zakzaky da matarsa sun bukaci Gwamnati ta biyasu kudin asarar da aka ja musu sakamakon cigaba da rike Fasfot ɗin su tsawon lokaci.

Labarai Makamanta