Kotu Ta Saki Dalibin Da Ya Wulakanta Aisha Buhari

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta janye ƙarar da shigar kan wani dalibin jami’ar tarayya dake Dutse, Aminu Mohammed, wanda ya kammala karatu a shekarar karshe bayan matsin lamba da kuma da alla-wadai da ga sassan kasar.

Da ya ke janye karar a yau Juma’a, lauyan masu shigar da kara, Fidelis Ogbobe, ya ce uwargidan shugaban kasa a matsayinta na uwa a kasa ta yanke shawarar janye karar, biyo bayan maganganu da ƴan Najeriya masu kishi su ka yi.

Ya dogara da Sashe na 108 karamin sashe na 2 (a) na Dokar Gudanar da Shari’a na Laifuka don nuna bukatar janye karar.

Da ya ke yanke hukunci kan lamarin, mai shari’a Yusuf Halilu na babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja, ya yaba wa Aisha Buhari bisa yadda ta ɗauki matakin yafe wa wanda ake tuhuma.

Yayin da ya ke bayar da takardar janye karar, alkalin ya yi kira ga iyaye da su rika sanya ido a kan ‘ya’yansu domin kaucewa sake faruwar hakan.

Muhammed, wanda ya fuskanci azabtarwa da kuma cin zarafi da suka hada da duka, ya fuskanci tuhume-tuhume na bata sunan uwargidan shugaban kasar Najeriya a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

A cewar wani rahoton ‘yan sanda, an kama Aminu Muhammed ne a Jami’ar Tarayya Dutse a ranar 18 ga Nuwamba, 2022 bayan Misis Buhari ta umurci tawagar ‘yan sanda da su bi diddigin sa.

Sannan an tsare shi a wani wuri da ba a san ko ina ba ne, aka hana shi ganawa da danginsa da lauyansa, wanda hakan ya saba wa dokokin kare hakkin bil’adama na duniya

Labarai Makamanta