Wata babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya a ranar Alhamis ta soke matakin hukumar tsaron farin kaya ta dauka na gayyatar gwamnan babban bankin Kasa CBN, Godwin Emefiele da kuma gurfanar da shi gaban kotu.
Alkalin kotun, Mai shari’a M.A. Hassan, ya yi la’akari da kudurin da kungiyar Incorporated Trustees of Forum for Accountability and Good Leadership ta gabatar a gabansa na tabbatar da hakkin Mista Emefiele, ya hana ‘yan sandan sirrin da cewa matakin zai kawo cikas ga muhimman abubuwan da Emefiele ya ke da su na hakkoki.
A wata takardar kotu da DAILY POST ta samu, an fitar da ‘Originating Motion’ a kan “Atoni Janar na Tarayya, Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Hukumar tsaron farin kaya da Babban Bankin Kasa.
Alkalin da ke jagorantar shari’ar ya kuma hana hukumar tsaron farin kaya ta daga ci gaba da tsangwama, wulakanci, kunyatarwa, barazanar dauri ko kuma tsare Mista Emefiele kan zargin badakalar kudaden ta’addanci da ayyukan zamba.
Kotun ta yi la’akari da hukuncin farko na umarnin babbar kotun tarayya da ke shari’a ma lamba FHC/ABJ/CS/2255/2022 da babban alkalin babbar kotun tarayya mai shari’a J. T. Tsoho ya bayar, ta caccaki rundunar ‘yan sanda tare da bayyana a matsayin daukar fansa duk wani ci gaba da hargitsi, tsoratarwa, barazana, ƙuntatawa na ‘yanci yin wani abu.
“Hakan zai zama, cin zarafi na ofishi, yunkurin kama Mista Godwin Emefiele da kuma wulakanta shi kan zargin badakalar kudaden ta’addanci da zamba.”
“Bisa la’akari da kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya da kuma dokar kare hakkin bil’adama na Afrika, (Ratification and Enforcement), hukumar DSS ta aikata abu ba bisa ka’ida ba wajen tunzura shugaban tarayyar Najeriya a kan Mista Emefiele game da mutuntawa na gudanar da aikinsa na doka da ya shafi fitar da manufofi da umarni na kudi don kare tsaron kasa da tattalin arzikin kasar,” in ji kotun.
You must log in to post a comment.