Kotu Ta Hana INEC Dakatar Da Rijistar Katin Zabe

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta hana hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC dakatar da rajistar katin zaɓe.

Hukumar dai ta sanya ranar 30 ga watan Yunin 2022, a matsayin ranar da za ta dakatar da rajistar masu zaben.

Sai dai kotun karkashin jagorancin mai shari’a Mobolaji Olajuwon ta bayar da umarni na wucin gadi kan daina yin rajistar har zuwa ranar 29 ga watan Yuni da za ta sake zama domin sauraron karar.

Mai shari’a Olajuwon ta yanke wannan hukunci na wucin gadi ne bayan sauraren karar da Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya ta shigar da INEC.

SERAP da sauran wasu masu fafutuka 185 suna shigar da karar Hukumar zaben a farkon wannan wata, suna neman kotu ta bayyana wa’adin da INEC ta sanya a matsayin haramtacce da ya ci karo da kundin tsarin Mulki.

Tare da bayyana shi a matsayin take hakkin ‘yan Najeriya na zaben, abin da suke so a dimokuradiyyance.

A cikin karar, SERAP ta nemi kotu ta hana INEC ko duk wani jami’inta ko dai wanda yake ikirarin aiki da ita dakatawa daga yin rijistar zabe a ranar 30 ga watan Yunin da muke ciki, ko kuma dage shi zuwa wata rana, har sai ranar da za a sake sauraren karar.

Yanzu dai an dage sauraren wannan kara har sai zuwa ranar 29 ga wannan wata na Yuni.

Ita kanta karar an shigar da ita ne bayan hukuncin da INEC ta yanke kara wa’adin kammala zabukan fidda gwani na jam’iyyun siyasa da kwanaki shida wato daga 3 watan Yuni zuwa 9 ga watan.

Sai dai kuma Hukumar ta ki dagawa al’umma kafa da ke yin rijista a intanet a ranar 30 ga watan Mayu, da kuma wadanda suke karbar katin zabe da wa’adin zai kare a karshen wannan wata.

Tun gabanin wannan kara dai al’ummar Najeriya ke kira ga Hukumar zaben ta kara wa’adin yin wannan rijista saboda mutanen da ba su da ita gaba daya, da wadanda ta su ta bata ko ta lalace ko kuma wadanda ke neman a sauya musu wurin zabe da dai sauransu.

Labarai Makamanta