Kotu Ta Bada Umarnin Kamo Tsohuwar Ministar Mai Duk Inda Take

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Babbar kotun tarayya dake zamanta a Abuja, ta bada umarnin kamo tsohuwar ministan Man Fetur, Diezani Alison-Madueke a duk inda ta ɓuya a duniya.

Alkalin kotun, mai Shari’a Bolaji Olajuwon, shi ya bada umarnin ranar Litinin, biyo bayan bukatar da lauyan hukumar yaƙi da cin hanci, (EFCC), Farouq Abdullah, ya gabatar.

A baya tsohuwar alƙalin kotun, Ijeoma Ojukwu, ta yi watsi da bukatar kamo Diezani, saboda gazawar EFCC wajen tabbatar da sammacin da aka aike wa tsohuwar ministan.

“A gani na sammacin da aka baiwa tsohuwar ministan zai baiwa ofishin AGF damar taso keyarta zuwa Najeriya.” Sai dai bayan canza wa Ojukwu wurin aiki zuwa kotun tarayya dake Kalabar, sai Shari’ar ta koma hannun Olajuwon.

Amma Abdallah, ya shaida wa kotun cewa ofishin Antoni Janar na ƙasa (AGF) na bukatar umarnin kotun domin hukumomin tsaro su samu damar kawo ta gaban alƙali ta fuskanci shari’a.

A zaman shari’ar na ranar Litinin, Abdallah ya bayyana wa kotu cewa duk wani yunkuri na dawo da Diezani Najeriya ya ci tura lokacin da lamarin ke hannun Ojukwu.

Da yake gabatar da bukatar da baki, yace akwai bukatar umarnin kame na kotu domin baiwa yan sandan ƙasa da ƙasa (INTERPOL) damar kamo ta zuwa Najeriya, ta fusƙanci tuhumar da ake mata a gaban kotu.

Daga nan sai alkalin ya ba da umarnin kama ta kuma ya ɗage zaman har sai lokacin da aka kama Diezani kuma aka gabatar da ita gaban kotu.

EFCC tace Diezani, wacce ke fuskantar sharia kan sama da faɗi da dukiyar ƙasa, ta buya ne a ƙasar Burtaniya, ta yi biris da ƙarar da aka kaita. A cewar hukumar EFCC, wannan umarnin ne zai baiwa INTERPOL dama su kamo ta, ofishin AGF ya cike sharuɗɗa a taso ƙeyarta zuwa Najeriya.

Labarai Makamanta