Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wata babbar kotun tarayya da ke zama a Minna, jihar Neja, ta bayar da umurnin kama babban hafsan sojin kasa Janar Faruk Yahaya bisa laifin rashin grimama kotu.
Mai shari’a Halima Abdulmalik, wadda ta yanke hukuncin ta kuma bukaci da a kulle Janar Yahaya a gidan gyara hali na Minna saboda saba ma wani umurnin kotu na ranar 12 ga watan Oktoba, 2022.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da wata babbar kotun da ke zamn ta a Abuja ta yanke wa sifeta-janar na ’yan sandan Najeriya hukuncin dauri na wata uku saboda kin martaba hukuncin kotu.
You must log in to post a comment.