Kotu Ta Bada Umarnin Iza Keyar Jaruma Sadiya Haruna Kurkuku

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewa Kotun Majistire, da ke zaman ta a Filin Jirgin sama na Kano, ta yanke wa wata jarumar Kannywood kuma shahararriyar mai amfani da kafar sadarwa ta instagram, Sadiya Haruna hukuncin ɗaurin watanni shida.

Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Muntari Dandago, ta yanke hukuncin ne ba tare da zaɓin tara ba.

An yanke wa Sadiya wannan hukuncin ne bisa kalaman ɓatanci da ta yi ga wani ɗan wasan kwaikwayo na Kannywood, Isah I. Isah a shafinta na Instagram.

An ruwaito cewa tun a ranar 16 ga watan Oktoba, 2019 a ka fara gurfanar da Sadiya a kotun.

Labarai Makamanta