Kotu Ta Ɗage Shari’ar Zakzaky Zuwa Karshen Watan Biyar

Alkalin Kotun dake saurarar shari’ar jagorar ‘yan Shi’ar Najeriya Sheikh Ibrahim Zakzaky a Kaduna Mai Shari’a Gideon Kurada a zaman da Kotun ta yi a yau Laraba ya ɗage cigaba da saurarar ƙarar har ya zuwa ƙarshen watan biyar ranar 25 ga watan Mayu dake tafe.

Da yake jawabi ga manema labarai jim kaɗan bayan kammala zaman shari’ar Dari Bayero, babban lauyan da ke jagorantar ‘shari’ar sirri’ na jagoran ‘yan Shi’ar da matarsa Zeenat, ya roki Babbar Kotu da ta dakatar da tuhumar ta yanke masu hukunci kamar yadda doka ta tanada.

Lauya Bayero, ya ce jihar ta rufe kararta bayan gabatar da shaidarta ta 15 a shari’ar. “Daya daga cikin addu’o’inmu shi ne kotu ta yanke hukunci a kan waɗanda ake tuhuma”.

Babu-Shari’ar-Gabatarwa, ta yi watsi da masu kariyar kuma ta hukunta wadanda ake tuhumar yadda ya dace da kuma yanke musu hukunci kamar yadda doka ta tanada,” inji shi.

Amma anashi bangaren Lauyan dake kare Shaikh Zakzaky, Femi Falana (SAN), ya fadawa manema labarai cewa tawagarsa za ta bude bada kariya a kan karar a ranar da aka ɗage.

Falana, wanda Marshall Abubakar ya wakilta, ya ce, bayan sun yi shawara kan fayil din wadanda ake tuhuma za su shigar da neman sallamar karar a gaban kotu.

A cewarsa, tun da farko mai gabatar da kara ya roki kotu da ta dakatar da tuhumar, ya kara da cewa, “Ya zuwa yanzu kuma kamar yadda shari’ar ta nuna, shaidu 15 na masu gabatar da kara ba su kafa hujja kan wadanda ake kara ba.”

A baya dai gwamnatin Jihar Kaduna ta tuhumi El-Zakzaky da Zeenat da aikata laifuka guda takwas wadanda suka hada da kisan kai, yin taro ba bisa ka’ida ba da kuma kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a, da sauran tuhume-tuhume.

Sai dai Shugaban ‘yan Shi’ar da matar sa sun musanta aikata laifukan lokacin da aka karanta masu tuhumar.

Labarai Makamanta