Korona Za Ta Zama Tarihi A Shekarar 2022 – Hukumar Lafiya

Hukumar Lafiya Ta Duniya ta bayyana cewa tana da yaƙinin cewa za a magance annobar korona a shekarar 2022 matuƙar ƙasashe suka haɗa kansu suka yi aiki kafaɗa da kafaɗa.

Shugaban Hukumar Lafiya Ta Duniya Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya bayyana hakan inda ya ce a halin yanzu akwai abubuwan da ake amfani da su domin kare kai da kuma maganin korona amma a cewarsa, iƙirarin kishin ƙasa da kuma ɓoye rigakafi da wasu ƙasashe ke yi ne ya haddasa ɓullar sabon nau’in Omicron na korona.

Mista Tedros ya bayyana cewa idan aka ci gaba da nuna bambanci, akwai barazanar cewa cutar za ta ci gaba da sauyawa ta hanyoyin da ba a yi zato ba.

Labarai Makamanta