Korona Ta Yi Tasiri A Harkar Fasahar Zamani – Pantami

Labarin dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, Ministan Sadarwa na Najeriya, ya ce cutar Korona ta kara habaka bukatar yin la’akari da fasahar zamani ta yadda za a magance kalubalen da annobar ta haifar.

An ruwaito cewa, ministan ya bayyana hakan ne a yayin taron gudanar da harkokin mulki na intanet na Afirka ta 2021 mai taken ‘Ci gaban sauye-sauyen fasahar zamani a Afirka ta fuskar rikici.’

Ministan ya fadi haka ne a lokacin da yake magana ta bakin wani darakta a hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC), wanda kuma shine mai ba shi shawara kan harkokin fasaha, Sahalu Junaidu. Pantami ya ce kalubalen da annobar ta haifar ya tabbatar da an samu karuwar bukatar ayyukan Intanet.

“Cutar Korona ta kara habaka bukatar rungumar al’adun fasahar zamani. Don haka, a matsayinmu na ’yan Afirka, daya daga cikin hanyoyin da za mu iya mayar da martani ga kalubalen da annobar ta jefa mu ita ce hanzarta sauya tsarin mu na fasahar zamani.”

Ministan ya ce, ya kamata a samo dabarun kawo sauyi na zamani ga Afirka kan muhimman ginshikai da dama, ciki har da fannin kirkire-kirkire na zamani da harkokin kasuwanci.

Labarai Makamanta