Korona Na Cigaba Da Kisa A Najeriya – NCDC

Hukumar takaita yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta bayyana cewa mutum 16 ne suka rasa rayukan su a dalilin kamuwa da cutar korona a kasar nan.

NCDC ta bayyana cewa a ranar Laraba mutum 8 ne suka mutu amma sai aka hada da mutum 8 din da suka mutu daga jihar Edo a ranar 8 ga Nuwanba.

A ranar mutum 65 ne suka kamu da cutar.

Zuwa yanzu mutum 212,894 ne suka kamu, an sallami mutum 204,675 sannan har yanzu mutum 5,297 ba dauke da cutar.

Cutar korona ta yi ajalin mutum 2,922 a kasar nan.

Yaduwar cutar

Legas – 77,915, Abuja-23,400, Rivers-12,772, Kaduna-10,124, Filato-9,866, Oyo-8,758, Edo-6,598, Ogun-5,374, Kano-4,380, Akwa-ibom-4,338, Ondo-4,573, Kwara-3,930, Delta-4,096, Osun-3,016, Enugu-2,776, Nasarawa-2,517, Gombe-2,695, Katsina-2,212, Ebonyi-2,048, Anambra-2,346, Abia-2,020, Imo-2,053, Bauchi-1,765, Ekiti-1,777, Benue-1,863, Barno-1,344, Adamawa-1,136, Taraba-1,250, Bayelsa-1,246, Niger-1,056, Sokoto-796, Jigawa-609, Yobe-501, Cross-Rivers-645, Kebbi-458, Zamfara-331, da Kogi-5.

Gwamnati ta yi wa mutum miliyan 5.7 allurar rigakafin cutar korona a Najeriya.

Shugaban fannin shriye-shirye, gudanar da bincike da lissafi na hukumar NPHCDA Abdullahi Garba ya bayyana cewa zuwa ranar 7 ga Nuwanba gwamnati ta yi wa mutum miliyan 5,770,899 allurar rigakafin korona a jihohi 36 da Abuja.

Ya ce daga ciki mutum miliyan 3,146,88 sun yi allurar rigakafin cutar zango na biyu a kasar nan.

Garba ya ce akwai kwalaben maganin rigakafin korona sama da miliyan takwas a kasar nan sannan har yanzu kasan na jiran wasu da za a kawo nan ba da dadewa ba.

Domin samun nasaran dakile yaduwar cutar gwamnati ta ce za ta yi wa mutum kashi 40% allurar rigakafin nan da karshen shekaran 2021 sannan ta yi wa kashi 70% rigakafin Nan da shekaran 2022.

Bayan haka Ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya yi kira ga mutane da su ci gaba da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar.

Ehanire ya ce yana da mahimmanci mutane su ci gaba da kiyaye sharuddan musamman bayan sun yi allurar rigakafin.

Ya kuma yi kira ga wadanda suka dara shekara 18 da su hanzarta zuwa wuraren da ake yin allurar rigakafin domin samun kariya daga kamuwa da cutar.

Ehanire ya ce tabbatar da ingancin ruwan maganin da ake amfani da su wajen yi wa mutane allurar rigakan a kasar duknan.

Labarai Makamanta