Korona: An Yi Kira Ga Buhari Ya Binciki Gwamnan Kogi

Ƙungiyar dake fafutukar kare haƙƙin bil’adama da saka ido kan al’amuran kuɗi (SERAP) ta roƙi shugaba Buhari ya yi bincike kan yadda aka karkatar da Naira Biliyan 4.5 kuɗin tallafin korona a Jihar Kogi.

Gwamnatin tarayya ta tura ma gwamnatin jihar Kogi Naira Biliyan 4.5 da ta samu daga rance, da kuma gudummuwa da ta samu don yaƙi da cutar COVID-19, kamar yadda aka ake wa sauran Jihohi.

SERAP ta bayyana haka ne a wani jawabi da ta fitar ranar Asabar inda ta roƙi shugaba Buhari da yaba Ministan shari’a da sauran hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa umarnin bincikar yadda aka ƙasafta kuɗin.

A jawabin SERAP ta ce: “Da zarar an sami ƙwaƙƙwarar shaida, duk wanda ake zargi a hukunta shi dai-dai da abinda ya aikata.”

A jawabin Mataimakin shugaban Ƙungiyar, Kolawole Oluwadare, ya sanya wa hannu ya bayyana cewa: “Bada umarnin ga ministan shari’a da kuma sauran hukumomin yaƙi da cin hanci doka ce a kundin tsarin mulkin ƙasar nan.” Kuma idan shugaba Buhari ya bada wannan umarnin to yana ƙara tabbatar da bayanin da ya yi lokacin rantsar dashi.

“Zan tabbatar da duk wasu ayyuka an gudanar da su yadda ya kamata a dukkan matakan gwamnati” inji Buhari.”Kamar yadda ka faɗa a wancan lokaci, ya zama wajibi gwamnatinka ta faɗaɗa yaƙi da cin hanci da rashawar da take yi zuwa dukkan matakan gwamnati uku da muke da su,” cewar SERAP.

Ƙungiyar tace ta damu da yawan korafe-korafe kan cin hanci da rashawa da kuma amfani da kuɗaɗen gwamnati ta inda bai kamata ba a dukkan jihohin Najeriya.

Ɗaukar ƙwaƙƙwaran mataki na yin bincike zai ƙara tabbatar da gaskiya da riƙon amanar gwamnati wadda ta ƙunshi jigar Kogi. “Zamu yi matukar jin daɗi idan aka ɗauki mataki akan korafin mu cikin kwanaki 14 da tura shi.

Idan kuma ba ayi komai ba bayan wannan lokacin, SERAP zata ɗauki matakin da doka ta tanadar wajen ƙalubalantar gwamnati har ta yi abinda ya dace.” Cewar SERAP.

SERAP ta tura cikakken bayanin da tayi a jawabinta zuwa ofishin ministan shari’a, Abubakar Malami, shugaban ICPC, Professor Bolaji Owasanoye, da kuma shugaban Hukumar yaƙi da cin hanci ta ƙasa (EFCC) Abdulrasheed Bawa.

Labarai Makamanta