Korar Malaman Kaduna: Malamai Za Su Tsunduma Yajin Aiki

Idan ba a manta ba gwamnatin jihar Kaduna ta kori malaman firamare sama 2000 a cikin makon jiya bisa dalilin basu zauna rubuta jarabawar kwarewa da gwamnatin ta shirya ba.

Cikin waɗanda aka kora har da Shugaban kungiyar na kasa Mista Amba Audu wanda shima bai zauna rubuta jarabawar ba.

Rahotanni sun bayyana Shugaban ƙungiyar ya umarci malamai da su kaurace wa jarabawar saboda babu dalilin sake rubuta irin wannan jarabawa bayan an taɓa rubuta irints a baya.

Dalilin haka Shugaban Malaman ya ki rubuta jarabawar da wasu malamai sama da 2000.

Sai dai kuma gwamnatin Kaduna a cikin makon jiya ta sanar da korar duk wanda bai rubuta jarabawar ba da ya haɗa da shugaban kungiyar na kasa.

Kungiyar malamai NUT ta ce ta na tare da shugaban ta kuma ba za ta yi kasa-kasa ba wajen tabbatar da cewa gwamnati ta dawo da malaman da ta kora.

Mataimakin shugaban ƙungiyar na kasa Kelvin Nwankwo ya ce ” Ko El-Rufai ya maida malaman aikin su ko kuma kungiyar malaman ta shiga yajin aiki na kasa baki ɗaya. Ba za mu bari a ci mutunci malamai haka kawai ba da sunan wai basu rubuta jarabawar gwaji.

” Za mu kare hakkin malamai da kuma shugaban mu da gwamnatin jihar ta ci wa mutunci.

Labarai Makamanta

Leave a Reply