Korar Fulani: Za Mu Yi Ramuwar Gayya A Arewa – Ƙungiyar Fulani

Sakataren Kungiyar samar da cigaban Fulani ta Ƙasa FULDAN Farfesa Umar Labdo, sannan kuma farfesa ne a bangaren siyasar musulunci a jami’ar Yusuf Maitama Sule dake jihar Kano, ya bayyana cewar muddin aka cigaba da korar Fulani a sashin Kudancin Najeriya babu shakka Fulani zasu yi ramuwar gayya a yankin Arewa.

A wata tattaunawa da jaridar Vanguard ta yi da shi ya bayyana tushen rikicin makiyaya da manoman kasar nan da kuma yadda za a shawo kan lamarin.

Kamar yadda yace, “Yadda aka bai wa Fulani kwanaki su tattara kayansu ba a kyauta ba, in dai har ana neman zaman lafiya. Akwai Yarabawa da suke damfara a yanar gizo da Ibo da suke sayar da miyagun kwayoyi a jihata wacce nake zama a arewa. Kuma suna zaune lafiya sana sana’o’insu babu wanda yace su kwashe kayansu.

“Don an san Fulani da garkuwa da mutane baya nufin duk wani bafulatani ne yake haka. Ai ba a yin jam’i. Duk wani bafulatani da aka samu da wannan laifin ai hukunta shi ya kamata a yi ba wai ace ya bar jiha ba.”

Ya kara da bayyana yadda Fulani suke da tsagwaron dukiya ta shanu amma sun gwammaci zama a daji,

Farfesa Labdo yace babu wani bafulatani nagari da zai fatattaki ‘yan kudu daga jiharsu, amma idan aka yi musu za su rama.

A cewarsa, “Bafulatani ba zai taba bai wa wani kabila lokacin barin jiharsa ba. Kuma matsawar aka cigaba da hantararsu, za su iya yin bore. Kuma gaba daya kasar za ta iya rudewa a rasa ta inda za a shawo kan lamurran.”

“Wajibi ne gwamnati ta tsaya tsayin-daka wurin ganin sun shawo kan wannan rikicin tun kafin al’amarin ya lalace gaba daya,” kamar yadda ya tabbatar.

Labarai Makamanta