Kungiyar cigaban Matasan yankin Arewa AYF ta mayar da martani da babban murya ga kalaman da aka ruwaito Babban Lauya Itse Sagay ke fadi na cewar dole Shugabancin Kasa ya koma kudu a shekarar 2023 bayan Buhari ya kammala wa’adin mulkinsa.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa da kungiyar ta fitar wadda ta samu sanya hannun Shugaban Ƙungiyar na kasa Alhaji Gambo Ibrahim Gujungu kuma aka rarraba ta ga manema labarai a Abuja.
Matasan sun kara da cewar abin takaici ne da damuwa kalaman babban Lauyan inda yake kiran Jam’iyya mai mulki ta APC da Jihohin Arewa 19 na ka da su tsayar da É—an Arewa takarar shugabancin kasa a 2023.
“Babban abin da ya kamata Lauya Sagay da masu ire-iren ra’ayinsa su sani shine, batun inda Shugabancin zai koma ko kudu ko arewa ba shine batu ba, abin da ake bukata shine samun Jajirtaccen Shugaba wanda zai kai kasar tudun mun tsira”.
Kungiyar Matasan Arewan sun kara da cewar a matsayin su na shugabanni ga matasan Arewa batun yankin da shugaba zai fito ba shine a gaban su ba, abinda ke gabansu shine samun shugaba nagari wanda zai ceto kasar daga mawuyacin halin da take ciki.
An ruwaito cewa Sagay na magana akan cewa Najeriya ba ta bukatar shugabanni matasa kamar Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, shin me ya sa Yahaya Bello ya tsone mishi ido.
Muradin mu a matsayin mu na Matasa shine Najeriya ta samun shugaban da ya dace daga kowane yanki ya fito a kasar.
You must log in to post a comment.