Ko Gawata Ba Za Ta Kusanci PDP Ba – Martanin El Rufa’i

Rahoton dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewa Gwamnan Nasiru Ahmad El Rufa’i ya mayar da martani ne ga ikirarin da kakakin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a 2023, Daniel Bawala, ya yi a shafinsa na Twitter.

A baya Bwala ya yi hasashen cewa, Nasiru El Rufa’i wanda tsohon minista ne na babban birnin tarayya Abuja zai fice daga jam’iyyar APC mai mulki nan ba da jimawa ba zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.

Bwala wanda har a kwanan baya dan jam’iyyar APC ne ya ce yana da kwarin gwiwar cewa El-Rufai zai shigo PDP kafin zaben 2023.

Sai dai a martanin da ya bayar a shafin sa na tsira Malam Nasiru El Rufa’i ya tabbatar wa duniya cewa yana nan daram a jam’iyyar APC ko gawarsa ba za ta kusanci PDP ba.

Labarai Makamanta