Ko Da Tsiya-Tsiya Sai Mun Ci Zabe A Kano – Shugaban APC

Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar Shugaban jam’iyyar APC na jihar Abdullahi Abbas ya sake ɓaro wata magana da ake ganin za ta iya haifar da rikici a zaɓen dake tafe musanman na Gwamna a jihar Kano.

“Ko da tsiya ko da tsiya-tsiya, ko ana ha-maza ha-mata, ko me za a yi, ko me zai faru, ko mai tafanjama fanjam sai mun ci zaɓe,” in ji Abdullahi Abbas.

Shugaban jam’iyyar APC ɗin, ya yi waɗannan kalamai ne a ranar Laraba yayin da suke ƙaddamar da kamfe ɗin takarar gwamna a Ƙaramar Hukumar Gaya.

A bayyane take ciyaman ɗin yana sane da cewa kalaman da yake yi ba su dace ba amma duk da haka sai ya faɗa.

Kafin ya fara ɓaɓatun sai da ya ce: “…ina tabbatar muku cewa wannan alama ce ta cin zaɓe. Wannan karon, duk da cewa an ce na daina faɗa, ko da tsiya…”

BBC ta nemi jin dalilinsa na yin waɗannan kalamai amma bai ɗaga waya ba sannan kuma bai amsa saƙon tes da muka tura masa ba.

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ne ya jagoranci taron, wanda ya samu halartar mataimakin gwamnan kuma ɗan takarar APC, Nasiru Yusuf Gawuna, da abokin takararsa Murtala Garo, da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya.

Kalaman nasa na zuwa ne a lokacin da hukumomi a cikin gida da ƙasashen waje ke kira ga ‘yan siyasa da guji kalaman tayar da fitina.

Labarai Makamanta