Kiwon Lafiya: Masana Sun Yi Kira Ga Jama’a A Kaduna

Daga Muhammad Sani Yusuf Nassarawa

Lafiya itace babbar jari ga kowanne dan Adam hakanne yasa masana harkokin lafiya ke bada shawarwari ta yaddda mutum zai kula da lafiyarsa.

wasu masana harkokin lafiya bisa koyarwar addinin Musulunci sun bayyana muhimmancin lafiya ga alumma
sunyi wannan kirane alokacin wata lacca da ta gudana a Ismail Bin Muhammad dage Unguwar Nassarawa kaduna

Tunda farko malami mai gabatar da laccar akan Muhimmancin lafiya wanda shine shugaban masu bada magani bisa koyarwar Addinin Islama Dr Yahaya Ishaq Sabil ya bukaci alumma da su dauki matakan kariya ga lafiyarsu Musamman ta abubuwan da suke ci ko sha ko kuma wurin Kwanciya da makamantansu

Shima a nasa jawabin Sakataren Kungiyar IPMPAN na jihar Imam Malam Musa Daee ya tabbatar da muhimmancin kula da lafiya Inda yayi hujja da hadin annabi dake magana akan gyaran zuciya cewa idan ta gyaru jiki ya gyaru haka kuma idan ta baci dukkan jiki ya lalace

Daga karshe Malam Rabiu Yunus ya ja hankalin masu saida magunguna ne da hotunan batsa ko kalaman batsa a cikin jama a inda ya bukacesu da suji tsoron Allah su daina domin hakan ba koyarwar addinin musulunci bane kuma yace sunanan za su dauki matakan yaki da irin wannan dabia ta batsa a tallan magani

Sanin kowane cewa babu wani abu mai muhimmanci da ya wuce lafiya ga Dan Adam inda koda yaishe masana lafiya ke gargadin a rika kokarin kula da lafiya ta kowacce fuska Domin lafiya itace Uwar Jiki

Labarai Makamanta