Kisan ‘Yan Arewa: Shiru A Arewa Ba Tsoro Bane – Babba Kaita

Sanata Ahmad mai wakiltar mazaɓar Katsina ta Arewa a majalisar Dattawa Sanata Ahmed Babba Kaita, ya yi kira da babbar murya akan a dakatar da kashe ‘yan arewa da ake faman yi a kudancin ƙasar nan cikin gaggawa, ba tare da ɓata lokaci ba.

Sanata Babba Kaita, ya cigaba da cewar, kamar dai yadda yan kudancin ƙasar nan ke walwala a Arewa, yakamta abar kowane ɗan arewa ya yi rayuwa cikin kwanciyar hankali a sashin Kudancin kuma yakamata abarsu su yi kasuwancin a kudanci kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar nan ya tanada.

Idan zaku iya tunawa, kwanakin baya, gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya gargaɗi ‘yan kudancin ƙasar nan dake rayuwa a arewa da kada su yi tsammanin kariya matuƙar aka cigaba da kashe ‘yan arewa a kudu.

Sanata Babba Kaita a wani taƙaitaccen jawabi da ya yi mai take ‘Arewa: babu sauran yin shiru’ ya ce a yanzun babban laifin ka shine ka zama ɗan arewa. Ba zamu zuba ido muna Kallo ana kashe mana Mutane a Kudu ba.

“Dan kogi ya tsaya cak, bashi ke tabbatar da cewa babu Kadoji a ƙarƙashinsa ba, kamar haka ne don ana cin mutuncin arewa ta hanyoyi da dama kuma mun yi shiru, hakan ba yana nufin ‘yan arewa ba su iya ramuwar gayya bane ko kuma basu san yadda ake buga wasan ba.”

Sanatan wanda yana goyon bayan kujerar shugaban ƙasa ta koma kudu a zaɓen 2023 ya ce ‘yan arewa sun yi shiru ne don kawai Najeriya ta cigaba da zama ƙasa ɗaya. Amma Kaita yace kowa ya yi da kyau to fa nan gaba shima zaiga dakyau, babu mai tantama akan wannan.

Ya ƙara da cewa a ko ina a faɗin duniya, gina ƙasa ba aikin mutum ɗaya bane, dole sai kowa ya bada haɗin kai, kuma Najeriya wani ɓangare ne na duniya.

Labarai Makamanta