Kisan ‘Yan Arewa Na Iya Haifar Da Basasa – Ƙungiyar Arewa

Ƙungiyar cigaban Matasan Arewa wato Arewa Youth Forum (AYF) a takaice, ta yi kira da babbar murya ga Shugaban ƙasa Buhari da ya yi gaggawar ɗaukar mataki daƙile rikicin da ya kunno a sashin Kudancin kasar na kisan ‘yan Arewa, domin kawar da yiwuwar faruwar yaƙin basasa a ƙasar.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata takardar sanarwa dake dauke da sa hannun Shugaban Ƙungiyar Alhaji Gambo Ibrahim Gujungu, kuma aka rarraba ta ga manema labarai a Kaduna.

Matasan sun bayyana cewar ba ƙaramin kuskure ba ne furucin da Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya yi ba na bada umarni korar Fulani daga jihar, wanda tabbas wannan babu abin da zai haifar da gagarumar matsala a ƙasar.

Matasan sun kara da cewar babu wata ƙasa da za ta iya samun nasara a hali na rashin tsaro, saboda haka alhakin gwamnatin l ne ta kare dukiya da rayukan jama’ar da suka zabe ta.

“Halin da ƙasa ke ciki nauyi ne da ya rataya a kafadun gwamnatoci baki daya na tarayya da jihohi, ba al’amari ba ne da za’a ɗora shi a bangare guda, bisa ga haka ya zama tilas e ayi dukkanin mai yiwuwa wajen magance matsalar.

“Muna kira da babbar murya ga gwamnati da cewar lallai a tabbatar an kama dukkanin waɗanda ke da hannu a rura wutar rikicin nan, a tabbatar a hukunta su domin rashin aikata hakan zake haifar da barazana ga al’umma baki ɗaya”.

Kungiyar ta kuma yaba gami da jinjina ga shugaban ƙasa Buhari na amsa kiran ‘yan Najeriya da ya yi na canza shugabanni tsaro, lallai wannan abin a yaba ne.

Sannan Matasan na Arewa sun kuma yaba matakan da sabbin shugabannin tsaron ke ɗauka na jajircewa wajen yaki da kawar da matsalar tsaro wadda ta ke addabar sashin Arewacin Najeriya.

Labarai Makamanta