Kisan Tinno: Hausa/Fulani Sun Koka Da Matakan Gwamnatin Adamawa

Hausa/Fulani a garin Tinno dake karamar hukumar Lamurde a jihar Adamawa sun koka da irin sakacin da gwamnarin jihar Adamawa ta yi wajen dakile rikicin kabilanci da ya barke tsakaninsu da ‘yan kanilar Choba, wanda aka dauki tsawon awanni goma ana yi amma babu wani dauki da jami’an tsaro suka kawo.

Daya daga cikin Hausawa mazauna yankin, ya bayyana cewa abin bakin ciki shine daga Tinno zuwa garin mataimakin gwamnan jihar Adamawa bai wuce kilomita biyar ba, amma duk da haka an gagara kawo musu dauki. Wanda suke zaton yin hakan ba ya rasa nasaba da cewa mataimakin gwamnan dan kabilar Choban ne. Sannan kuma sauran kabilun dake yankin sun taya na Choba yakar Hausawan ne, inda suka fito da manyan bindigu suna harbi.

Sannan koda aka ce Gwamna Fintiri ya ziyarci garin bai karaso garin Tinnon ba domin ganewa idon sa irin barnar da aka yi, ya tsaya ne a inda jama’a suka yi gudun hijira a cikin wata makarantar firamare dake garin Lamurde.

A jiya ne dai aka samu rikicin kabilanci tsakanin kabilar Choba da Hausa/Fulani, wanda aka samu asarar rayuka da dama.

Related posts