Kisan Sardauna: Zai Yi Wuya Inyamuri Ya Zama Shugaban Kasa – Okupe

Tsohon hadimin shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan, Doyin Okupe ya bayyana cewa har yanzu Arewa bata yafewa Inyamurai kisan Marigayi, Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto ba.

Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda yace, lamarin da ya faru a shekarar 1966 an yi imanin cewa Soja Inyamuri ne ya aikatashi.

Doyin dake da niyyar tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023 ya bayyana cewa amma Inyamurai zasu iya zama da Arewa a yi Sulhu. Yace idan aka yi sulhu aka yi alkawari to zai iya hakura da takarar da zai yi, amma idan ba’a samu irin wannan sulhu ba, bazai Hakura ba.

Ya tabbata a tarihi tun bayan kisan da Inyamurai ƙarkashin jagorancin Chukuma Nzeogwu suka yi wa Sardauna da sauran manyan Arewa a shekarar 1966, wata gaba ta shiga tsakanin Inyamurai da jama’ar Arewa, lamarin da ake ganin shi ya haddasa musu rashin samun Shugabanci ƙasar har yanzu.

Labarai Makamanta