Kisan Jama’a Ya Fi Tsanani Akan Garkuwa Da Mutane – Gumi

Babban malamin addinin Islama mazaunin garin Kaduna Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Mahmoud Gumi ya kwatanta garkuwa da yara ‘yan makaranta da ‘yan Bindiga ke yi a matsayin wani abu mai sauki idan aka kwatanta shi da kisan da ‘yan Bindigar ke yi na tayar da Ƙauyuka baki ɗaya.

Dr. Ahmad Abubakar Mahmoud Gumi ya sanar da hakan ne yayin tattaunawa da yayi da bangaren Pidgin na na gidan Rediyon BBC ranar Litinin.

Malamin ya ce ganawarsa da ‘yan bindiga ya haifar da ɗa mai ido domin kuwa yanzu ‘yan bindigan suna kiyaye rayukan jama’a.

Kamar yadda Gumi yace: “Garkuwa da yaran makaranta karamin laifi ne saboda daga karshe za a yi sasanci da iyayensu kuma yanzu ‘yan bindiga suna kiyaye rayukan jama’a.

“Kafin nan, aikin ‘yan bindigan shine zuwa garuruwa, kakkabe jama’a da kashe su. A yanzu haka zan iya cewa da’awa ta yi aiki kuma muna da burin kawo karshen ‘yan bindigan Zamfara da sauran jihohi.

“’Yan bindiga yanzu suna kiyaye rayuka kuma kai musu hari janyo magana ne.”

Labarai Makamanta