Kisan Hanifa: Uwargidan Shugaban Kasa Ta Kai Ziyarar Ta’aziyya

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewa Uwar gidan shugaban ƙasa, Aisha Muhammadu Buhari, ta kai ziyara jihar domin jajantawa gwamnati da al’umma bisa kisan Hanifa Abubakar da rasuwar fitaccen Malami, Dakta Ahmad Bamba.

A wani taron manema labarai da ta yi a gidan gwamnati, Aisha tace ta kawo ziyara ne a ƙashin kanta domin ta yi ta’aziyya ga iyalan mutanen biyu, wanda ta bayyana rashin su a matsayin babban rashi a ƙasa.

“Na zo nan jihar ne a karan kaina domin jajantawa gwamnan jihar Kano da matarsa, Sarkin Kano da kuma sauran mazauna jihar bisa rashin fitaccen malami, Sheikh Ahmad Bamba da Hanifa Abubakar.”

“Muna addu’a kuma muna fatan za’a yi mata adalci. A matsayina na uwa ina da ‘ya’ya da jikoki dake karatun Firamare yanzu haka, sun yarda da malaman su, muma iyaye mun amince da su.” “Don haka idan har yara ba zasu samu kwanciyar hankali a makarantun su ba, hakan na nufin cewa al’umma ta canza zuwa wani abu daban. Ina ganin ya dace a ɗauki mataki don kare makamancin haka nan gaba.”

Da yake jawabin godiya, gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya tabbatar wa uwar gidan shugaban ƙasa cewa gaskiya zata yi halinta domin dole a hukunta mai laifi.

“Hanifa ɗiyar mu ce kuma ɗiyar kowane ɗan Najeriya ce. Mun damu sosai kuma mun ji daɗin wannan ziyara tun daga Abuja.” “Hatta lokacin da lamarin ya faru kin fito fili kin yi magana cewa kina fatan gwamnati zata ɗauki matakan tabbatar da an hukunta waɗan da suka aikata haka.”

Labarai Makamanta