Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Kisan Hanifa: Ba Zan Bata Lokaci Wajen Sa Hannun Zartar Da Hukunci Ba – Ganduje

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar yace ba zai bata lokaci ba wajen zartar da hukuncin kashe Abdulmalik Tanko, idan aka kawo shi kan teburinsa.

A ranar Litinin an ruwaito cewa gwamnan ya yi alƙawarin bin dokar da tsarin mulki ya tanadar wajen zartar da hukuncin kisa kan Tanko, bayan kotu ta tabbatar.

Ganduje ya yi wannan furucin ne yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya tare da mataimakinsa, Nasuru Yusuf Gawuna, shugaban masu rinjayi na majalisa, Labaran Abdul da ƙusoshin gwamnati zuwa gidan iyayen Hanifa.

“Mun samu kyakkyawan tabbaci daga kotun dake suararon ƙarar cewa za’a yi adalci kan lamarin. Babu ƙashin da ya fi karfin a taunasa.” “Duk wanda aka tabbatar ya aikata wannan ɗanyen aiki, to za’a kashe shi ba tare da ɓata lokaci ba.

A bangaren mu, tuni muka fara shirye-shirye.” “Doka tace bayan kotu ta yanke hukuncin kisa, gwamna ke da ikon zartar da hukuncin kan wanda ya aikata laifin. Dan haka ina tabbatar muku ko daƙiƙa ɗaya ba zan ɓata ba.”

Game da yanayin tafiyar shari’ar, gwamnan ya kara jaddada cewa ba za’a tsaya wani kace nace ba wajen yanke hukunci da yi wa Hanifa da iyalanta adalci. Kazalika kan abin da ya faru da makarantar da Hanifa ke karatu, Ganduje ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta yi abin da ya dace.

Exit mobile version