Kisan Goronyo: Shugaban ‘Yan Kasuwar Arewa Ya Yi Allah Wadai

Biyo bayan hari da aka kai a ksauwar goranyo dake jihar Sokoto wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da jikkata jama da dama a jihar Sokoto.

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar Arewacin Najeriya Alhaji Muhammed Ibrahim 86 ya nuna alhininsa tare da yin Allah wadai da wannan hari da ‘yan bindiga suka kai a kasuwar goronyo wanda a cewarsa wannan abun takaicine.

Muhammed Ibrahim ya bayyana haka ne a zantawarsa da manema labarai a Yola fadar gwamnatin jihar Adamawa.

Ibrahim 86 ya kuma jajantawa gwamnatin jahar Sokoto karkashin jagorancin Aminu Waziri Tambuwal da mai alfarma Sarkin Musulmi Abubakar Sa’ad tare da ‘yan kasuwar jihar harma da alummar jihar ta Sokoto bisa wannan lamari da ya faru.

Ya kuma kirayi gwamnatin tarayya dana jihar dama hukumomin tsaro da suyi dukkanin abunda suka dace domin ganin an kawo karshen irin wadannan hare hare domin ganin an samu cigaban harkokin kasuwanci dama bunkasa tattalin arzikin kasanan baki daya.

Alhaji Ibrahim 86 ya kuma yi addu’ar Allah madaukakin sarki ya jikan wadanda suka rasu ya kuma baiwa wadanda suka jikkata lafiya.

Harwayau ya shawarci ‘yan Najeriya da su cigaba da addu’oi domin neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo karshen dukkanin kalubalen tsaro a fadin Najeriya baki daya.

Ya kirayi yan Najeriya da su cigaba da baiwa gwamnati dama hukumomin tsaro hadin kai da goyon baya domin ganin sun cimma burinsu na kare rayuka dama dukiyoyin al’umma baki daya.

Labarai Makamanta