Kisa Ne Maganin ‘Yan Bindiga Ba Sulhu Ba – El Rufa’i

Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El Rufa’i ya sake jaddada matsayarsa kan cece kucen da ake yi na yin afuwa ga ‘yan Bindiga inda ya ce masu wannan tunani suna da karancin hangen nesa babu wata hikima ko tasiri na yin sulhu da ‘yan Bindiga.
“Mu kashe su kawai, idan ya so waɗanda suka rage sai mu duba yiwuwar karɓar tubansu”.

El-Rufai ya yi waɗannan batutuwa ne yayin wani taron tattaunawa da aka gudanar ranar Juma’a, 19 ga Fabarairun 20121 kan makomar Najeriya mai taken The Fierce Urgency of Now: Tactics and Strategies to Pull Nigeria from the Brink, wanda aka gudanar a Jihar Legas.

An sha jin gwamnan wanda ya taɓa jagorantar wani kwamitin jam’iyyarsu ta APC kan sake fasalin Najeriya, yana bayyana cewa ya kamata a sake duba fasalin ƙasar domin ƙara wa jihohi ƙarfin iko.

A jawabin nasa na ranar Juma’a, El-Rufai ya ce ‘yan sandan Gwamnatin Tarayya ba za su isa ba.

“Abu ne mai mahimmanci a samar da tsarin tsaro na tarayya da na jiha da na cikin al’umma. ba mu da isassun ‘yan sanda. ‘Yan sandan Gwamnatin Tarayya kaɗai sun yi kaɗan,” a cewarsa.

Wani abu da gwamnan ya taɓo shi ne maganar kashe-kashen da ‘yan bindiga ke aikatawa a kowace rana, abin da ya bayyana da cewa Najeriya “na rasa ƙarfin ikon da take da shi a matsayinta na ƙasa”.

A cewarsa: “Najeriya a matsayinta na ƙasa ta gaza kare muradunta da kimarta a matsayinta na mai samar da tsaro da kare haƙƙi da kuma tabbatar da doka.

“Wannan ne dalilin da ya sa ‘yan bindiga ke kawo mata wargi duk da ƙarfin ikonta kuma ta hanya mafi muni da tsoratarwa.”

Kazalika, El-Rufai ya ce akwai buƙatar a sauya tsarin shari’a a Najeriya, ta yadda za a bai wa kotunan Jihohi ƙarfin ikon gudanar da wasu shari’o’i.

“Abin da nake bayar da shawara a nan shi ne, a rage wa tsarin shari’a a matakin tarayya ƙarfi nan take, ba gobe ba, ba anjima ba.

“Tsarin shari’ar da ake bi yanzu yana yin jinkirin da ke kawo tsaiko wurin maganin matsalolinmu, har ma ‘yan ƙasa su riƙa tunanin tuni har an saki masu laifin ma, kuma hakan ƙarfafa wa masu niyyar aikata laifi gwiwa.”

‘A bai wa jihohi ikon mallakar arziƙinsu’

Gwamnan ya ƙara da cewa tun da dai jihohi ne ke da ikon mallakar filaye ko ƙasar da ke garuruwansu, to ya kamata su mallaki arzikin da ake samu daga ma’adanan da ke ƙasashen nasu – amma su biya haraji ga Gwamnatin Tarayya.

“Dole ne mu gyara kundin tsarin mulki domin tabbatar da mallakar man fetur da iskar gas da ma’adanai da ke jihohi, waɗanda da ma su ne ke da iko kan ƙasa bisa dokar ƙasa.”Su kuma sai su biya Gwamnatin Tarayya haraji.”‘A rage kashe kuɗi wurin tafiyar da gwamnati’.


Kafin gwamnan ya ƙare jawabinsa sai da ya bayar da wasu shawarwari da yake ganin su ne mafita ga ɗorewar Najeriya, ciki har da rage kuɗin tafiyar da gwamnati da ƙara azama wurin karɓar haraji da mutunta haƙƙin kowane ɗan ƙasa da sayen makamai ga jami’an tsaro.

“A yi gagarumin yunƙuri wurin rage kuɗin tafiyar da gwamnati a matakin tarayya da ƙaramar hukuma ta hanyar haɗe ma’aikatun da ke da aiki iri ɗaya, sannan kuma a jingine batun ƙirƙirar wasu gwamnatoci ko hukumomi saboda gaba.”

Labarai Makamanta