Kisa Ne Mafi Cancanta Ga ‘Yan Bindiga – Sarkin Katsina

Labarin dake shigo mana daga Jihar Katsina na bayyana cewar Mai martaba Sarkin Katsina Abdulmumini Kabir, ya ce hanya ɗaya ta kawo ƙarshen ayyukan yan bindiga ita ce duk wanda aka kama a kashe.

Sarkin ya yi wannan furucin ne a fadarsa dake Katsina, yayin da mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya kai masa ziyara. Yayin ziyarar, Osinbajo, ya shaida wa Sarkin cewa gwamnati ta ayyana yan bindiga a matsayin yan ta’adda, domin baiwa jami’an tsaro damar ɗaukan tsauraran matakai a kansu.

Yayin da yake martani kan haka, Sarkin na Katsina ya bayyana cewar “Ina cikin damuwa, haka gwamna Masari, amma na yi matukar farin ciki a yanzu da aka ayyana su a matsayin yan ta’adda.” “Saboda haka yanzun zaku kama ku kashe, domin ita ce kaɗai mafita tun da shirin tattaunawar sulhu ya ci tura.”

Basaraken ya koka da cewa, “Ta ya mutum zai kashe rayuka 20 zuwa 30 amma a tura shi gidan gyaran hali? Ba zai haifar da ɗa mai ido ba, domin duk randa ya fito zai sake komawa ruwa ne.”

Sarkin ya kuma yi kira ga mazauna jihar su koma ga Allah, su masa biyayya kamar yadda ya umarta, sannan su kyautata wa junan su.

Labarai Makamanta